Inda za ka san waƙa tsari ne na Allah kuma ɗabi’a ce ta ɗan adam shi ne idan ka ɗauki yaro ɗan shekara ɗaya ko biyu da ka sa masa waƙa za ka ga yana nuna alamar zai yi rawa, yana nuna jin daɗinsa, sannan idan ka dubi duk wani dattijo za ka ga ya haddace wata waƙa ta zamaninsa” inji Malamin.