Game Damu
An kafa Majalisar Malamai ta Ƙasa ranar 11 ga Muharram 1400AH (23 ga Agusta, 1980) don zama wakiliyar musulmi wajen magance ƙalubalen da ke fuskantar addini a Najeriya. Babban burinta shi ne ƙarfafa haɗin kai da zumunci tsakanin musulmi, samar da al’umma mai tsoron Allah, haɓaka wa’azi, rubuce-rubuce, da ayyukan musulunci, tare da inganta koyarwar addini daga matakin firamare har zuwa jami’a.